16 Satumba 2025 - 22:38
Source: Quds
Yemen: Ta Kai Hari Da Makamai Masu Linzami linzami Tel Aviv

Kakakin Rundunar Sojin Yaman: Mun kai hari da makami mai linzami na Falasdinu 2 a Tel Aviv. 

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Mai magana da yawun rundunar ƙasar Yamen Birgediya Janar Yahya Saree ya ce a wannan farmakin an yi amfani da makami mai linzami nau'in "Falasɗinu 2" wajen kai hari kan wani muhimmin wuri a birnin Jaffa da ke yankunan da aka mamaye.

Saree ya kuma sanar da cewa, aikin ya samu nasarar cimma manufofinsa tare sanya tserewar "miliyoyin 'yan sahayoniyawa zuwa mafakar matsuguni.

Ya ce wannan farmakin na goyon bayan al'ummar Palastinu ne da ake zalunta a Gaza da kuma mayar da martani ga wuce gona da iri da gwamnatin yahudawan sahyoniya ke kai wa a Yaman.

Ya kuma kara da cewa dakarun kasar Yemen sun sake kai wani farmakin da jiragen saman kasar suka kai, inda suka kai hari a tashar jirgin saman Ramon da ke yankin Umm al-Rishrash (Eilat) da ke kudancin kasar Falasdinu da Isra'ila ta mamaye.

Kakakin sojojin kasar Yemen, yayin da yake kara sabunta kiran da yake yi ga Al'ummar Musulmin ƙasashen duniya da su sauke nauyin da ke wuyansu wajen taimakawa 'yan'uwansu a Gaza da ake yi wa kisan kare dangi da kakaba yunwa da raba su da muhallansu, ya yi gargadin cewa: Ta'addancin yahudawan sahyoniya zai kai ga kasashe daban-daban matukar dai al'ummomi da gwamnatoci ba su dauki wani mataki na tsayayye su tsaya tsayin daka wajen fuskantarsu ba.

Daga karshe ya jaddada cewa dakarun kasar Yemen za su ci gaba da gudanar da ayyukansu har sai an daina kai hare-hare a kan Gaza tare da dage wannan kawanyar.

Your Comment

You are replying to: .
captcha